Kaza da shanshani - African Storybook Project
Transkript
Kaza da shanshani - African Storybook Project
Kaza da shanshani Plan Niger - Projet NECS - Usaid, Avec la contribution du and Avec la contribution du Comité ASL Winny Asara Hausa Kaza da shanshani abokai ne. Amma kullum suna takara tsakaninsu. Wata rana, sai suka yi niyyar wasan ƙwallon ƙafa don sanin wa ya fi kwaninta tsakani su biyu(2). 1 Sai suka shiga filin ƙwallon ƙafar kuma suka fara wasan. Kaza tana da gaugawa amma shanshani ta fi ta gaugawar. Kaza ta harba ƙwallon nesa amma kuma shanshani tana aika ƙwallon neza ƙwarai fiye inda na kazar zai je. Ganin haka, sai kaza ta fara hassala. 2 Ƴan takarar biyu (2) sun yi niyyar su je bugun da kai sai mai tsoron gida. Da farko shanshani ita ce mai tsaron gida wato gola kenan. Kaza ta saka ƙwallo ɗaya rak cikin raga. Sai aka juya, kaza ta zama gola mai tsaron gida. 3 Shanshani ta harba ƙwallo, kuma ta saka a raga. Shanshani tana gwaninta kuma tana saka ƙwallon. Shanshani ta saka ƙwallon har da kai. Shanshani ta saka ƙwallon biyar (5). 4 Kaza ta hassala da rishin nasarar da ta yi. Kaza ba ta iya wasa ba. Shanshani ta yi ta dariya saboba abokiyarta ta hassala wajen wasa. 5 Sai kaza ta buɗe babban bakinta ta haɗiye shanshanin. 6 Lokacin da kaza tana shigowa gida, sai ta gamu da uwar shanshani. Sai ta ce mata, “ba ki ga ɗiyata ba?” Kaza ba ta amsa mata ba. Uwar shanshani ta damu. 7 Sai uwar shanshani take ji wata ƙaramar murya tana cewa: “Ki agaje ni uwata!” Shanshani take faɗi. Uwar shanshani ta duba kewayenta da kyau. Muryar nan da cikin kaza ta fito. 8 Uwar shanshanin ta yi ihu “Ki yi amfani da duk azirinki ɗiyata!” Shanshani ta saki wani wari. Sai kaza ta fara jin wani ciwon ciki. 9 Kaza ta yi gyatsa. Kuma ta yi kaki. Ta yi attishewa kuma take ta tari, take tari. Shanshani bai ciyuwa! 10 Kaza ta yi ta tari sai ta kako shanshanin da yake cikin cikinta. Shanshanin da uwarta sun tafi sun ɓoye cikin wani icce. 11 Tun daga shi, kaza da shanshani ba su shiri. 12 You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way: Kaza da shanshani Author - Winny Asara Adaptation - Plan Niger - Projet NECS - Usaid, Avec la contribution du and Avec la contribution du Comité ASL Illustr Illustration ation - Winny Asara Language - Hausa Le Level vel - Longer paragraphs © African Storybook Initiative, 2014 Creative Commons: Attribution 4.0 Sour Source ce www.africanstorybook.org
Benzer belgeler
Tayaka murnar sayan Sony Ericsson W760i. Siririyar waya mai salo
Karanta Jagororin don aminci da ingantaccen amfani
da babukan garanti mai iyaka kafin amfani da
wayarka.
Wayarka ta hannu tana da damar saukewa, ajiyewa
da tura žarin abun ciki, misali, sautunan ri...